Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan muhimman wurare 23 na kasar Siriya a cikin sa’o’i 24 da suka gabata
Majiyoyin watsa labaran Siriya sun bayyana cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare har sau 23 kan wasu muhimman wurare a sassa daban-daban na kasar da nufin durkusar da kasar a fannin ci gaban zamani.
Majiyoyin sun kara da cewa: A cikin sa’o’i 23 da suka gabata a jiya Asabar, sojojin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan wurare daban-daban har 23 kuma 12 daga cikinsu cibiyoyin na’urorin rada ne mafiya muhimmanci a kasar Siriya a tsaunin Qasioun, baya ga wasu yankuna tare da lalata su da manyan makamai masu linzami wadanda suka haddasa manyan fashe-fashe.
Majiyoyin sun jaddada cewa: Tuni rundunar sojin Golani suka mamaye dukkan wuraren radar, inda suka janye daga gare su mintuna kadan kafin a kai farmakin, wanda ke nuni da kasancewar hadin baki kai tsaye da jiragen da suka kai hare-haren.
Abin lura a nan shi ne cewa, sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-hare sama da 350 a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata a kan wasu wurare da dama na soji da binciken ilimi a kasar Siriya.