Sojojin Isra’ila Sun Zafafa Kai Hare-haren A Gaza Da Lebanon

Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-haren a Gaza lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 20 tare da jikkata wasu da dama a sansanin

Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-haren a Gaza lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 20 tare da jikkata wasu da dama a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Zirin.

Bayan hakan, sojojin Isra’ila sun kai harin bam a asibitin al-Awda, lamarin da ya rusta da mutane da dama.

Tun soma farmakin na Isra’ila a Gaza a ranar 7 ga Oktoba 2023, Falasdinawa a kalla 43,603 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 102,929 suka jikkata.

A wani lamari na daban, akalla mutane 14 ne sukayi shahada, yayin da wasu 15 suka jikkata, lokacin da wani harin da Isra’ila ta kai kan wani gida a arewacin kasar Labanon.

A Lebanon din dai, adadin wadanda suka rasu ya kai a kalla mutane 3,189, yayin da wasu 14,078 suka jikkata, sakamakon hare-haren da Isra’ilar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments