Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun bude wuta kan gungun falasdinawa dake neman agaji a yankin gaza, inda akalla mutane 4 suka mutu, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata.
Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da sama da mutane paladinawa 1000 dake neman agaji da sojojin Isra’ila suka kashe a kusa da inda ake raba kayan agaji. Dake karkashin kulawar amurka da isra’ila a yankin na Gaza.
Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akalla yankin gaza yana bukatar manyan motocin agaji 500 zuwa 600 a duk rana domin biyan bukatun su na yau da kullum, sai dai har yanzu Isra’ila na ci gaba da rusa gidaje a yankin Gaza.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ne sojojin Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a yanin Gaza, inda suka yi watsi da kiran da kasashen duniya suka yi na tsagaita bude wuta, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 64,756, mafi yawanci mata da kananan yara.