Sojojin Isra’ila Sun Kama Falasdinawa 2 A Yammacin Kogin Jodan

sojojin isra'ila sun kai samame a gabar yammacin kogin jodan inda suka yi amfani da hanyaki mai sa hawaye kana suka kama mutum 2

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin isra’ila sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa matasa falasdinawa da fararen hula tare da kama wasu matasa guda biyu a garin aqraba dake kudu masu gabashin Nablus a gabar yammacin kogin jodan

Rikicin ya barke ne tsakanin falasdinawa da sojojin Isra’ila a wata mamaya da suka kai a kauyen madama dake kudancin Nablus, a yankin al-mugayyir dake arewa masu gabashin Ramallah ma sojojin isra’ila sun kama wasu matasa falasdinawa a gidansu.

Sojojin isra’ila da yahudawa yan share wuri zauna sun kai hare hare kan falasdinawa a yankin gaza da sauran yankunan da aka mamaye a yammcin kogin Jodan, a baya bayan nan ma yahudawa yan share wuri zauna sun kai hari kan matasa a gabar yammacin kogin jodan, inda suka kunna musu wuta a gonakinsu da sauran kayayyakinsu,

Wani bafalasdini ya mutu a wani hari da jiragin saman isra’ila ya kai a kan cincirindon jama’a a yankin gaza tare da jikkata wasu da dama dake wajen, daga ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 zuwa yau yankin yammacin kogin jodan ya fuskanci hare hare na wuce gona da iri daga sojojin isra’ila inda suka yi wa dubban falasdinawa kisan gilla da tilastawa miliyoyi barin gidajensu ba shiri

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted