Rahotonni daga Siriya sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama fiye da sau 250 kan yankuna daban-daban na kasar Siriya a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Majiyoyin watsa labaran Siriya sun bayar da rahoton cewa: A yammacin jiya litinin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan tashar jirgin saman Qamishli ta runduna ta 54 a yankin Tartab da ke arewa maso gabashin kasar Siriya.
Haka nan majiyoyin sun bayyana cewa: Farmakin da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan kasar ta Siriya sun fi shafar bangarorin karfin soji na sojojin Siriya ne musamman cibiyoyin kula da harkokin soji, filayen jiragen saman yakin soji, cibiyoyin binciken soji, barikokin tsaro, barikokin sojin Siriya, tashoshin jiragen ruwa da sauran muhimman wurare a kasar.