Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare kan Siriya

Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan yankuna daban-daban na kasar Siriya a yammacin Juma’a. Rahotanni cikin gida sun ruwaito cewa jiragen

Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan yankuna daban-daban na kasar Siriya a yammacin Juma’a.

Rahotanni cikin gida sun ruwaito cewa jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare akalla 20 a wajen garuruwan Damascus, Daraa da Hama, inda suka auna wuraren sojoji da ma’ajiyar kaya.  

Hare-haren sun hada da wani sansanin sojojin Syria da ke kusa da kauyen Shatha da ke Hama, hedkwatar tsohuwar bataliyar sojojin Syria da ke arewacin Damascus, da kuma sansanonin soji a Dera.

Fashe-fashe sun afku a Damascus da kewaye, ciki har da Harasta, inda wani farar hula ya mutu.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa an kai hari a wasu yankuna a babban birnin kasar a karon farko.

Tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disambar 2024, kasar Siriya ta kasance karkashin mamayar Isra’ila.

Da sanyin safiyar Juma’a ne jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a yankin da ke kusa da fadar shugaban kasa a Damascus, wanda shi ne hari na biyu da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kai a cikin wannan mako.

Hukumomin Isra’ila sun kare harin a matsayin goyon baya ga al’ummar Druze, wadanda ke fafatawa da wasu masu dauke da makamai da HTC ke marawa baya a kusa da Damascus a wani sabon tashin hankali na kabilanci a karkashin mulkin HTC.

Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments