Sojojin Isra’ila Sun Harbi Salameh Har Sau 9 A Gidan Kurkuku

sojojin isra'ila sun harbi babban kwamanda a kungiyar hamas har sau tara a inda ake tsare da shi

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin hki sun harbi babban kwamanda a kungiyar izzud den qassam bangaren soji na kungiyar hamas har sau 9 a gidan yari a inda ake tsare da shi shi kadai cikin matsanancin yanayi bayan da yayi ikirarin cewa sai ya kashe ministan yakin isra’ila ben-gvir,

lamarin ya faru ne tun a ranar 28 ga watan satumba bayan da minista itmar ben-gvir ya fada dakin da ake tsare da Salameh a gidan yarin ganot tare da sojoji dauke da makamai, inda ya fada masa cewa ina so in kashe ka, kuma sai na ga karshenka

An haifi salama ne a shekara ta 1971 a sansanin yan gudun hijira na khan yunus a yankin gaza daga iyalan da aka kora daga gidajensu a lokacin nakba a shekara ta 1948 kuma ana tsare da shi a gidan yari tun a shekara ta 1996, kuma an yanke masa hukunci kisa har sau 48,daya daga cikin hukunci da ya fi tsanani da aka taba yankewa, saboda jagorantar hare-haren daukar fansa kan isra’ila na kashe kwamandan kungiyar Qassam yahya Ayyash

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted