Sojojin Jamhuriyar Musulunci na Iran suna gudanar da atisaye da makaman tsaro sararin samaniya kiran gida
Sojojin kasar Iran sun fara gudanar da atisayen soji da na’urorin tsaron sararin samaniyar kasar a shiyar yammacin kasar da kuma arewacin a safiyar yau lahadi.
A wata sanarwa da ya aike wa tashar talabijin ta Al-Alam kafin fara atisayen sojin, kwamandan rundunar tsaron sararin samaniyar kasar Iran Birgediya Janar Ali Reza Sabahi Fard ya ce: Wannan atisaye yana fayyace yanayin tsaro ne na hakika, kuma zai hada da atisayen tunkarar barazanar tsaro ta sama da amfani da makamai masu linzami da kuma yakin lantarki.
Birgediya Janar Sabahi Fard ya jaddada cewa: Za su yi amfani da na’urorin tsaron sararin samaniya da aka kera masu yawa a cikin kasa. Yana mai bayyana cewa: Wadannan kayan aiki ya fi zama nagartattun hanyoyin kariya a duniya.
Dangane da sakon wannan atisaye, kwamandan sojojin tsaron sararin samaniya na Iran ya bayyana cewa: Wannan atisaye yana aikewa ne da sakon zaman lafiya ga kasashen da suke makwabtaka da Iran.
Birgediya Janar Sabahi Fard ya bayyana cewa: Kasashen yankin ne ke da alhakin wanzar da zaman lafiya da tsaron yankinsu, ba baki ‘yan kasashen waje ba.