Sojojin HKI Suna Cigaba Da Kai Hare-hare A Yankin Tulul-Karam

Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna

Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna yi.

Bugu da kari, sojojin mamayar suna cigaba da kama Falasdinawa a wannan yankin,inda a daren jiya su ka kutsa cikin unguwanni mabanbanta.

Har ila yau, sojojin mamayar sun kwace gidajen Falasdinawa da dama da suke a kusa da sansanin Tul-kram, da mayar da su zama sansanonin soja.

Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da ‘yan sahayoniyar su ka tilastawa yin hijira daga sansanonin Tul-Karam da Nuru-Sahmsh, sun kai 10,000.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa, adadin mutanen da su ka yi shahada a cikin kwanaki 21 na hare-hare sun kai 11, yayin da wasu gwammai su ka jikkata.

Mazauna yankin kuwa suna cewa, ‘yan sahayoniyar sun killace yankin, sun kuma yanke ruwa da wutar lantarki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments