Sojojin HKI Sun Yi Wani Sabon Kisan Kiyashi A Gaza

Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar  Falasdinawa 57 Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai

Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar  Falasdinawa 57

Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai hari ne akan makarantar ” Fahmi al-jarjawi” wacce take a yankin al-Darj’ a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.”

 Harin ya yi sanadiyyar konewar gawawwakin shahidan da kuma tashin gagarumar gobara a makarantar da  ‘yan hijira Falasdinawa suke ciki.

 Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa  daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa ya haura dubu 53 da 939.

Haka  nan ma’aikatar ta ce; Wadanda su ka jikkata kuwa a wannan tsakanin sun kai dubu 122 da 797.

Sojojin HKI sun shelanta yaki ne akan yankin Gaza da zummar murkushe kungiyar Hamas, sai kuma kwato fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya, lamarin da ya zuwa yanzu babu wanda ya tabbata.

Daga farkon yakin ne dai kungiyar Hamas ta sanar da cewa, ta hanyar tattaunawa ne kadai za a iya yin musayar fursunoni.

Ya zuwa yanzu kuwa an yi musayar fursunonin a tsakanin bangarorin biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments