Sojojin HKI Sun Yi Kisan Kiyashi A Yankin Shuja’iyya

Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi

Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.

 Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar ta Shuja’iyya.Dama tun da safiyar Laraba wasu Falasdinawan 50 sun yi shahada a wannan unguwa ta Shuja’iyya dake cikin birnin Gaza.

Wasu majiyoyin Falasdinawa sun ambaci cewa: Sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren da manyan bindigogi a kusa da masallacin; UMMU HaBIBAH, da kuma kasuwar sayar da kekune a yankin Qaizan a kudancin Khan-Yunus.

A gefe daya,majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa; Da akwai Falasdinawa miliyan daya da aka kora daga gidajensu da karfi.

Kungiyoyin fararen hula sun ambaci cewa; A kalla da akwai mutane miliyan daya da aka tilastawa ficewa daga gidajensu zuwa wasu yankuna. Kungiyoyin suna kokarin kafa sansanonin tsugunar da wadanda aka tilastawa yin hijirar.

Wata matsalar da ake fuskanta a Gaza ita ce yadda ‘yan sahayoniyar su ka hana yi wa kananan yaran yankin allurar riga-kafin shan inna, lamarin da yake yin barazana sake dawowar cutar bayan kawar da ita.

Bayanin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ya ambaci cewa tun daga 2023 zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 50,886, yayin da wadanda su ka jikkata adadinsu ya kai 115,875.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments