Kafafen yada labarai da dama sun bada labarin cewa sojojin HKI sun mamaye wasu karin yankuna a kasar Siriya kusa da tuddan Golan na kasar a dai-dai lokacinda yan tawayen ‘Hai’at Tahrirusham’ ta kwace iko daga hannun Bashar Al-Asad.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bada labarin cewa a karon farko tun shekara 1947 an ga motovin HKI a kudancin kasar Diriya. Sannan sun kutsa cikin kasar har zuwa kilomita 14 a lardin Qanaitara mai makobtaka da tuddan Golan. Sannan sun mamaye yankin Jabal Shiek sun kuma samar da shinge yankin da suka kebe a kewaye da shi.
Labarin ya kara da cewa HKI ta yada sojojinta a dukkan yankunan da sukamamaye.
A wani labarin kuma a jiya ne majalisar dokokin HKI ta amince da mamayara wasu yankuna a kasar ta Siriya. Wasu kafafen yada labaran yahudawan sun bayyana cewa firay ministan HKI Benyamin Natayanhu ya zo har yankin duddan Golan na kasar Siriya a jiya inda ganewa kansa yaddda gwamnatin Asad ta fadi, da kuma yadda babu sojojin kasar siriya ko guda a kan iyakokin kasashen biyu.