Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da jiragen ruwan yake daga tekun medeteranina sun cilla wuta kan garuruwan Beit –Lahia, Rafah da kuamKhan Yunus inda suka kashe da dama ko suka kaisu ga shahada.
Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun sake mamayar yankin Netzarim wanda ya raba arewa da kudancin zirin gaza a yau Alhamis.
Ya zuwa yanzu yawan falasdinawa da suka yi shahada ya kai 49,547 tun fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, sannan yawan wadanda suka ji raunikuma ya karu zuwa 112,719 kamar yadda ma’aikatar lafiya ta zirin gaza ta bayyana.
HKI ta koma yaki bayan da ta yi watsi da tsagaita wuta da kungiyar Hamas, ita kadai a ranar Talanta da ta gabata.
A cikin kwanaki uku da suka gabata HKI ta kashe Falasdinawa kimani 500 a yankin Gaza. Inda kasha 2/3 daga cikinsu mata da yara ne.