Sojojin HKI sun kashe wata yar jarida mai aikiwa tashar talabijin ta “Qudsul- Yau” a wani harin da ta kai a zirin gaza.
Islam Abed ta hadu da ajalinta a lokacinda jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan birnin gaza a jiya Lahadi da yamma. Wanda ya kara yawan yan jaridan da HKI ta kashe a wannan yakin
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ‘Al-asksal Yau’ tana yin All..wadai da HKI, sannan ta kara da cewa, kissan Islam Abed ba zai kawo karshen rahotannin da yan jaridu suke aikawa duniya dangane da ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da suka mamaye ba.
Haka ma ofishin tashar talabijin ta Al-aksa a gaza ta bayyana cewa kissan Islam Abed ya kara bakanta HKI a duniya, a kan kasa wacce tafi ko wace kasa a duniya kissan yan jarida don kada duniya ta ji gaskiyar abinda yake faruwa a kasar Falasdinu ba.