Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Siriya a daren jiya.
Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya nakalto majiyar gwamnatin kasar na cewa, hare haren na daren jiya dai, sun fada kan yankunan Al-Arida da Dabussiyeh na kan iyakar kasar Siriya da Lebanon.
Labarin ya kara da cewa mashigar Dabussiyya da kuma Jussiyah suna cikin lardin Homs na kasar Siriya ne, sai kuma Al-Aradi wanda yake cikin lardin Tartous mai iyaka da kasar ta Lebanon.
Ministan sifiri na kasar Lebanon Ali Hamieh ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan wadannan kofofin shiga kasar Siriya daga kasar Lebanon, guda uku ne bayan da aka bada labarin tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hizbullah a jiya da dare.
Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta bayyana cewa jami’in agajita guda ya yi shahada a hare-haren yahudawan na daren jiya, kuma wasu da dama sun ji Rauni.