Sojojin HKI Sun Bude Wuta Kan Jami’an Diblomasiyyar Wadanda Suka Je Jenin

Sojojin HKI sun bude wuta nag aske kan jami’an diblomasiyya na wasu kasashen Turai wadanda suke kokarin shiga sansanin yan gudun hijira na Jenin don

Sojojin HKI sun bude wuta nag aske kan jami’an diblomasiyya na wasu kasashen Turai wadanda suke kokarin shiga sansanin yan gudun hijira na Jenin don galin yadda rayuwa take tafiya a cikinsa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jamilan diblomasiyya wadanda suke ziyarar sansanin yan gudun hijiran a yau Laraba dai sun hada da jakadun kasashen  Austria, Brazil, Bulgaria, Canada, Chile, China, Masar, Faransa, India, Japan, Jordan, Lithuania, Mexico Morocco, Poland, Portugal, Romania, Rasha, Sri Lanka, Spain, Turkey, tarayyar Turai (EU), da kuma Burtaniya.  Tare da su akwai wakilai daga wasu kasashen duniya da kuma yan jarida.

Ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinawa ne ta shiryawa wadannan kasashen ziyara zuwa wannan yankin na yamma da kogin Jordan don ganewa idanunsa yadda HKI ta maida rayuwan falasdinawa a yankin yamma da  kogin Jordan da aka mamaye.

Ma’aikatar ta aiwatar da irin wannan ziyarar zuwa sansanin yan gudun hijira na  Tulkaram da ke yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.

A wasu hotunan bidiyo da aka nuna, an ga yadda wasu jami’an diblomasiyya suke nuna fushinsu da yadda sojojin yahudawan sukabude masu wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments