Kafafen yada labarai sun bayyana cewa sojojin HKI suna ci gaba da mamayar kasar Siriya, kuma ya zuwa yanzun sun kafa sansanin sojoji a Lardin Qunaitara na kasar ta Siria, sannan sun kara mastowa daga kan iyakar kasashen biyu har zuwa wani wuri wanda baifi kilomita 25 daga babban birnin kasar ta Siriya wato Damascus.
Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya ce sojojin HKI sun isa dotsen Hermon, sun kuma kwace yankin duddan Golan gaba dayansa.
Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa, tankunan yaki na HKI sun kai wani wuri kilomita 3 daga garin Qatna, wanda kuma yake tazarar kilimota 20 kacal daga babban birnin kasar Damascus.
Labarin ya kara da cewa zuwa jiya Laraba sojojin HKI sun mamaye garuruwa da kauyuka masu yawa a kudancin kasar ta Siriya wadanda suka hada da Aama, Baqa’sm, al-Reemeh, Hinah, Qal’a, Jandal, al-Husseiniyah, Jita, da kuma al-Khashab wadanda suke kudancin birnin Damascus.
Sannan ta sama kuma, sun kai hare hare har 350 a wurare daban-daban a kasar ta Siriya inda suka wargaza sansanonin sojojin ruwa da na sama da kuma rumbunan ajiyar makamai na kasar.
Labarin ya kammala da cewa wuraren da ta kaiwa hare-haren, mafi yawa su suna cikin biranen Damascus, Homs, Tartus, Lantakia, da kuma Palmyra.