A daidai lokacin day akin Gaza ya cika kwanaki 430, ‘yan gwgawarmaya a Gaza sun sanar da kai wani hari akan sojojin mamaya a arewacin Gaza wanda ya yi sanadiyyar halakar sojoji 3.
Ita ma majiyar sojojin mamayar ta tabbatar da cewa an kashe musu sojoji 3 da kuma jikkata wasu 18. Kafar watsa labaru ta “ Libon Shitash Ish” ta Hibru, ta sanar da cewa; Wani yanayi mai tsanani ya faru a Jabaliya wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin da kuma jikkatar wasu, bayan da aka kai hari akan wata motar daukar abubuwa masu fashewa.
Rahoton ya cigaba da cewa, wata mota mai dauke da abubuwa masu fashewa ta isa yankin Jabaliya, sai wani daga cikin ‘yan gwgawarmaya ya harbo makami akan motar, da hakan ya yi sanadiyyar tarwatsewarta. Nan take sojoji 3 su ka halaka yayin da wasu 18 kuma su ka jikkata.
Bugu da kari, an ga jirage masu saukar angulu na soja suna sauka a arewacin Gaza, domin jigilar sojojin da su ka halaka da kuma jikkata zuwa asibiti.
A daya gefen sojojin HKI suna cigaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi a Gaza, tare da kai wa asibitin “Indonesia” hari. Rahotanni sun ambaci cewa 6 daga cikin masu jiyya a asibitin sun jikkata.
A can yankin Rafah ma dai sojojin HKI sun kai wasu hare-haren akan gidajen mutane tare da rushe su baki daya.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta ce; ‘Yan sahayoniyar suk kashe mutane 50 da jikkata wasu 84 a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Ya zuwa yanzu jumillar wadanda su ka yi shahada sun kai 44,758, sai kuma wasu 106,134 da su ka jikkata.