Sojojin HKI 12 ne suka halaka ko suka ji rauni wani harin da dakarun hamas suka kai masu a zirin gaza. A dai-dai lokacinda suke kai mummunan hare- hare kan Falasdinawa don nufin mamayar birnin Gaza.
Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar labarain na yahudawan na fadar haka takumakara da cewa sojojinsu 4 ne suka halaka a yayinda wasu 8 suka ji rauni a wani harin da kungiyoyin Falasdinawa suka kaiwa sojojinsu a birnin Gaza.
Rahoton ya kara da cewa hare-haren da Falasdinawan suka kai yakamata a ce wuri ne maiaminciga sojojin yahudawan a Gaza.
Wannan yana faruwa ne a dai dai lokacinda dakarun falasdinawa sun shaalwashin kare mutanensu a gaza. Wadanda suke fuskantar kissan kare dangi mafimuni a cikin yan kwanakin da suka gabata.