Kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga Chadi, inda ta fara janye wasu jiragen yaki guda biyu daga kasar, kwanaki kadan bayan da Faransa ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Paris.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, kakakin rundunar sojin Faransa Col. Guillaume Vernet ya sanar da cewa, wasu jiragen yaki samfarin Mirage 2000-D sun bar sansani na Faransa da ke N’Djamena, inda suka doshi sansanin sojojin sama na Nancy a gabashin Faransa.
“Wannan shi ne matakin farko na maida kayan aikin Faransa da aka jibge a N’Djamena,” in ji shi, kuma ajandar ficewar zai dauki makonni da yawa kafin a kammala.
Vernet ya jaddada cewa, ana ci gaba da tattaunawa da jami’an kasar Chadi dangane da lokaci da kuma hanyar da Faransa za ta janye sauran dakarunta 1,000 a kasar ta Afirka, da kuma ko dukkansu za su fice.
Kasar Chadi ta kasance kawa ga Faransa a yakin da ake yi da ta’addanci, kuma daya daga cikin kasashen karshe da Faransa ta girke sojoji a yankin, bayan da aka kore su daga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
A wani mataki na ba-zata da gwamnatin kasar Chadi ta dauka a ranar 28 ga watan Nuwamba, ne ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Faransa, inda ta bayyana hakan a matsayin wani sauyi ga kasar tare da jaddada cewa, matakin zai bai wa kasashen Afirka damar sake daidaita huldar abokantaka daidai da manufofin kasashensu.