Gwamnatin kasar Slovakia zata sake bude tattaunawa da kasar Rasha a mako mai zuwa, a dai dai lokacinda sabani yake kara fadi tsakanin kasashen turai da kuma kungiyar tsaro ta NATO.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen tv ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa, ministan harkokin wajen kasar Slovakia ya bada sanarwan cewa kwamitin hadin giwa ta tattalin arziki, kimiya da fasaha tsakanin Rasha da Slovakia zai zauna a Mosco tare a ranar 26 ga watan Octoba da muke ciki. Kuma wannan shi ne taron kwamitin na farko tun bayan fara yaki a kasar Ukraine a shekara ta 2022.
Ministan ya kara da cewa a taron kwamin hadin giwan za’a tattauna aiki tare tsakanin kasashen biyu dangane da Makamashin Nukliya, ayyukan Noma, matsalolin yanayi, wasanni da al-adu.
Wannan taron ya yi burus da baton takunkuman dorawa man kasar rasha takunkumai na kasashen EU zuwa shekara ta 2027.
Slovakia dai tana ci gaba da sayan mai da gas na kasar Rasha, kuma tana son ci gaba dahakan har bayan shekara ta 2027. Duk tare da matsayin EU da NATO a kan hakan.