Siriya Da Rasha Sun Fatataki ‘Yan Ta’adda A Idlib

Jiragen saman yakin Rasha da na Siriya sun kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Siriya domin

Jiragen saman yakin Rasha da na Siriya sun kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Siriya domin fatattakar ‘yan ta’addar da ke samun goyon bayan kasashen waje.

Sojojin Siriya da na Rasha sun kai farmaki kan maboyar kungiyoyin ‘yan ta’adda a Idlib a ranar Lahadi, yayin da suke kara kai hare-hare a yankunan da ‘yan ta’addan ke rike da su a arewa maso yammacin Siriya kusa da kan iyaka da Turkiyya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da sojojin kasar ta Siriya suka fara kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda a kudu maso gabashin Idlib a ranar Alhamis din da ta gabata, inda suka sake kwace iko da kauyen Jobas tare da tilastawa mayakan barin kauyukan Dadikh da Kafr Battikh da ke gabashin Idlib.

A ranar Laraba ne ‘yan ta’addan da ke karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham suka kaddamar da wani gagarumin hari a lardin Aleppo da Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Siriya, inda suka kwace yankuna da dama.

Tun daga wannan lokaci ne sojojin gwamnatin Siriya ta fara gwabza kazamin fada da ‘yan ta’addar domin samun galaba a kansu.

Tun a watan Maris din shekara ta 2011 ne dai kasar ta Siriya ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda daga kasashen ketare, inda Damascus ta ce kasashen yammacin turai da kawayen su na yankin suna taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’adda su yi barna a kasar ta Larabawa.

Kasar Rasha tare da Iran, na taimakawa sojojin Syria a yakin da ake gwabzawa a kasar da ke fama da rikici, musamman ta hanyar ba da taimako ta sama ga hare-haren kasa kan ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments