Shugabannin Kungiyar ECOWAS Na Taronsu Karo Na 66

Yau Lahadi ake gudanar da babban taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 66 a birnin Abuja na Najeriya.      Batutuwa da dama ne ke

Yau Lahadi ake gudanar da babban taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 66 a birnin Abuja na Najeriya.     

Batutuwa da dama ne ke cikin ajandar taron, da suka hada da ficewar da kungiyar kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso suka sanar a ranar 29 ga watan Janairu.

Kasashen Sahel sun tsaya kai-fata akan anniyarsu ta fiyewa daga kungiyar duk da yunkurin shiga tsakani.

Taron zai kuma tattauna inda aka kwana game da shirin samar da kudin bai daya na kasashen ECOWAS, inda ministan kudi na Najeriya zai bayyani.

Taron wanda ake sa ran shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat zai halarta, za’a tattauna batun aiwatar da rundunar ‘yan sandan Afirka ta Yamma don yaki da ta’addanci.

A wannan Asabar, shugaban kasar Mali kuma shugaban kungiyar AES, Janar Assimi Goïta, ya ba da sanarwar daukar dukkanin matakan da suka dace na samar da shoge da fice tsakanin ‘yan asalin Afirka ta Yamma a cikin kasashen na hadakar AES ba tare da biza ba ga duk ‘yan kasashen mambobin kungiyar ta ECOWAS.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments