Shugabannin kasashen Larabawa sun tattauna kan batun Gaza dama halin da ake ciki yankin.
Bisa gayyatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, an gudanar da taron ‘yan uwantaka na yau da kullun a birnin Riyadh a ranar Juma’a inji kamfanion dilancin labaren kasar na SPA.
Taron ya samu halartar sarki Abdullah II na Jordan, da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da shugaban kasar Masar, da Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa hyan, da Sarkin Kuwait Sheikh Meshal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, da kuma Yarima mai jiran gado kuma firaministan kasar Bahrain Yarima Salman bin Hamad Al Khalifa.
Taron ya ba da damar tuntubar juna kan batutuwa daban-daban na shiyya-shiyya da na kasa da kasa, tare da mai da hankali musamman kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falastinu da kuma mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa a zirin Gaza.
Shugabannin sun yi maraba da gudanar da taron gaggawa na kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira na Masar a ranar 4 ga watan Maris, mai zuwa.