Shugaban (WHO) Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Harin Isra’ila A Yemen

Shugaban Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da wasu ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya sun tsallake rijiya da baya a wani hari da Isra’ila ta kai kasar

Shugaban Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da wasu ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya sun tsallake rijiya da baya a wani hari da Isra’ila ta kai kasar Yemen a ranar Alhamis

Isra’ila ta kai harin ne a babban filin jirgin sama na Sanaa, lokacin da shugaban na WHO da tawagarsa, ke filin jirgin saman Sanaa lamarin da rahotanni ke cewa ya yi sanadin mutuwar mutum akalla shida.

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Dr Tedros ya ce ya je Yemen ne “domin tattauna yadda za a sako ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ake tsare da su da kuma duba yanayin wahalar da al’umma ke ciki” a kasar.

Kan batun hare-haren da Isra’ilar ta kai a filin jirgin saman na Sanaa, ya ce: “An lalata hasumiyyar aikawa da karbar bayanan zirga-zirgar jirage, da dakin jira na fasinjoji – waɗanda ba su da nisa daga inda muke – har ma da titin tashin jirage.

“Dole sai mun jira an gyara barnar da aka yi kafin mu bar kasar,” in ji Tedros.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments