Shugaban Tunusiya Ya Jaddada Bukatar Raya Nahiyar Afirka Ta Hanyar Bunkasa Tattalin Arzikinta

Shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa: Afirka na bukatar sabuwar hanya don tunkarar son ran ‘yan mulkin mallaka Shugaban kasar Tunusiya Qa’is Saeed ya bayyana

Shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa: Afirka na bukatar sabuwar hanya don tunkarar son ran ‘yan mulkin mallaka

Shugaban kasar Tunusiya Qa’is Saeed ya bayyana a ranar Alhamis cewa: Tunisiya tana alfahari da hadin kan kasashen Afirka, kuma ta tsaya tsayin daka kan burin kafa kungiyar tarayyar Afirka mai inganci, duk kuwa da kalubalen da nahiyar ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula, fadace-fadace, laifuffukan safarar bil adama, da rashin samar da muhimman abubuwan rayuwa.

A jawabin da ya gabatar a wajen bude taron baje kolin kasuwanci a kasar Aljeriya karo na 4, Saeed ya ce: “Nahiyar Afirka na da dimbin arziki, amma a lokaci guda tana fuskantar talauci da ke sanya matasanta shiga cikin hanyoyin safarar mutane.”

Ya ci gaba da jaddada cewa, “Afrika na bukatar sabuwar hanya, musamman a karkashin tsari, da zai gudanar da aiki a asirce da ayyuka da zasu sarrafa tattalin arzikin Afirka”, a cewar rahoton Sputnik.

Ya kara da cewa “kudin da aka gabatar yana da alaka da makomar Afirka da kuma bil’adama kuma dole ne ya hada da bangarori daban-daban”, yana mai kira ga hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka.

Shugaban kasar Tunisiya, Qais Saeed, ya kuma jaddada a cikin jawabin nasa, cewa: Wajibi ne a tallafa wa al’ummar Falastinu don dawo da cikakken ‘yancinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments