Jaridar ” Up Isra’el” ta buga labarin cewa; shugaban cibiyar Ayyukan Agaji A Gaza” wacce ke karkashin Amurka da Isra’ila” ya yi murabus saboda abinda ya kira rashin gaskiya da ‘yanci a cikin Shirin.
Jaridar ta ambato Jake Wood yana cewa; Ba abu ne mai yiyuwa ba a aiwatar da Shirin agaji a Gaza, sannan kuma a ce za a yi aiki da ka’idojin ‘yan’adamtaka, tsaftar aiki, da cin gashin kai, da abubuwa ne wadanda ba zan taba ja da baya a kansu ba.”
Wood ya yi kira da a yi ayyukan gabatar da kayan agajin a cikin yankuna masu yawa na Gaza,a kuma a yi aiki da dukkanin hanyoyin gabatar da taimako.”
Wood ya bayyana cewa; Tun watanni biyu da su ka gabata ne aka tuntube shi domin ya jagoranci wannan cibiyar,saboda kwarewar da yake da ita a fagen ayyukan agaji, sannan ya kara da cewa: ” Daidai da sauran mutane masu yawa a duniya, na firgita, na kuma yi bakin ciki saboda yadda na ga ake fama da yunwa a Gaza,sannan kuma a matsayina na jagora a fagen ayyukan agaji na ji cewa nauyi ne da ya rataya a wuyana in yi abinda zan iya saboda rage wahalhalun da mutane suke cki.”
Jaridar ta “Up-Isra’el” ta kuma ce; Ajiye aiki da Wood ya yi, babban ci baya ne ga Isra’ila, kuma ya zuwa yanzu babu tabbacin ko wannan cibiyar za ta yi aikinta.”
Da akwai alamar tambaya akan ayyukan cibiyar wacce ba a adade da kafa ta ba, sannan kuma babu cikakkiyar masaniya akan inda ta samo kudin da su ka kai dala miliyan 100.
MDD dai ta ce ba za ta shiga cikin ayyukan agaji a Gaza ba, matukar ba za a bi dokokin kasa da ka sa ba.”