Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni da a sake duba farashin kuɗin aikin Hajjin 2026, domin rage nauyin da zai rataya kan alhazai, sakamakon yadda Naira ke kara karfafa kan Dalar Amurka a kasuwa.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya mika umarnin Shugaban kasan ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), inda ya ce a cikin kwanaki biyu hukumar ta fitar da sabon tsarin farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin Kasar a yanzu.
Da yake jawabi a fadar shugaban kasa bayan taro da shugabannin NAHCON, Shettima ya ce ya zama dole a samu hadin kai tsakanin gwamnoni da jami’an hukumar alhazai domin tabbatar da tsarin farashi mai sauki da adalci ga maniyyata.
Shi ma Sakataren NAHCON, Dr Mustapha Mohammad, ya ce wannan mataki na shugaban kasa zai kara yawan maniyyata a bana, yana mai jaddada cewa “karancin farashi zai ba da damar musulmi da dama su sami damar aiwatar da wannan rukuni mai muhimmanci na addinin Musulunci.”