Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen kisan kiyashin da take yi a Gaza. Ya yi kira da a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma Qudus a matsayin babban birninta tare da baiwa Falasdinawa ‘yan gudun hijira ‘yancin komawa kasarsu ta gado.
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yana mai jaddada cewa: A yau, tsarin rayuwa da tattalin arzikin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya ratsa ta wasu kasashen musulmi, kuma lokaci ya yi da kasashen musulmi za su tilasta wa wannan gwamnatin mamaya ta hanyar yanke shawarar gama-gari don kawo karshen killace Gaza.