Shugaban Majalisar Dokokin kasar Labanon Nabih Berri ya mika ta’aziyyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei dangane da shahadar shugaba Raeisi da mukarrabansa.
Nabeh Berri tare da wata babbar tawagar gwamnatin Lebanon da ta hada da ministoci da manyan jami’ai da ‘yan majalisa sun halarci janazar marigayi shugaba Ibrahim Ra’isi.