Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran ya isa kasar China domin halartar taron shugabannin ma’aikatun shari’a na kasashen da suke mambobin kungiyar Shangai karo na 20.
Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhsini Eiji wanda shi ne shugaban ma’aikatar shari’a ta jamhuriyar musulunci ta Iran, ya nufi kasar China a yau Litinin domin halartar taron kungiyar Shangai wanda shi ne irinsa karo na 20.
Gabanin barinsa filin saukar jiragen sama na “Mehrabad” Eiji ya bayyana muhimmancin yin aiki a tare a tsakanin ma’aikatun shari’a na kasashen mambobin kungiyar Shanghai sannan ya kara da cewa: ” Taron na shugabannin ma’aikatun shari’a karo na 20 na kungiyar Shangai za a yi shi ne a garin Hangatsho, za kuma mu hatarta ne a karkashin bunkasa diflomasiyya ta fuskar shari’a da kuma fadada alaka ta fuskar doka a karkashin wannan kungiya ta Shangai.
Ita dai wannan kungiyar ta Shangai,mambobinta suna da mutanen da su ne kaso 40% na al’ummar duniya,ana kuma daukarta a matsayin kungiyar yanki mafi girma. Kasashen kungiyar dai suna aiki ne domin bunkasa alakar da take a tsakaninsu a fagagen tattalin arziki, siyasa, tsaro,soja da kuma sharia.