Shugaban Kungiyar ECOWAS  Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau

Shugaban kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kuma shugaban kasar saliyo Julius mada Bio yace ya tattauna da shugaban mulkin soji da ya

Shugaban kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kuma shugaban kasar saliyo Julius mada Bio yace ya tattauna da shugaban mulkin soji da ya yi juyin mulki a kasar Guinea Bissau , a kokarin da suke yi na ganin an yi aiki da kundin tsarin mulki a yankin na yammacin Afrika.

A cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X bio ya fadi cewa ganawar ta su ta zo ne bayan kudurin da kungiyar ta ECOWAS ta fitar a taron da ta gudanar kan irin mataken da zaa dauka game da batun juyin mulki da aka yi a kasar Guinea Bissau a makon jiya.

Shiga tsakani a rikicin kasar Guinea Bissau ya zo ne sakamakon rashin zaman lafiya na siyasa da kuma tarihin juyin mulkin soja a kasar, tun bayan samun yanci kai a shekara ta 1974 , guinea Bissau ta sha fama da yankewar harkokin mulkin demukuradiya akai –akai.

Tshon shugaban Nigeria Goodlock Jonathan wanda ya jagoranci tawagar ECOWAS don sa ido kan yadda zaben ke gudana ya sanya alamar tambaya game da hakikanin juyin mulki da sojoji suka yi , yace wani shiri ne tsakanin shugaban kasar Embalo domin kaucewa rashin nasara a zaben da aka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments