Shugaban Kasar  Turkiyya Ya Bukaci Zaman Tattaunawa Da Takwaransa Na Kasar Siriya

Shugaban kasar Turkiyya ya fitar da wata sabuwar sanarwa game da muradin sa na ganawa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad Shugaban kasar Turkiyya Rajab

Shugaban kasar Turkiyya ya fitar da wata sabuwar sanarwa game da muradin sa na ganawa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya jaddada shirinsa na ganawa da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, lamarin da ke nuni da cewa yana jiran martani daga gwamnatin Siriya.

Erdogan ya shaida wa manema labarai kafin tafiyarsa zuwa Amurka domin halartar zaman taron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Suna son gudanar da zaman tattaunawa shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad domin daidaita alakar da ke tsakanin Turkiyya da Siriya, kuma a yanzu suna son yin taro da Bashar al-Assad don haka suna jiran martanin da ya dace daga gwamnatin Siriya.

Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa: A shirye suke don ganin an samu hadin kai tsakanin kasashen musulmi da al’ummominsu, kuma suna fatan hakan zai faru albarkacin wannan taro.

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana cewa: An nada ministan harkokin wajen kasarsa Hakan Fidan don shirya wani taro da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, wanda za a yi a wata kasa ta daban.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments