Shugaban kasar ta Sudan Janar Abdulfattah al-Burhan ya ziyarci Masar domin ganawa da takwaransa Janar al-Sisi, inda su ka tattauna halin da ake ciki a Sudan, da kuma matsalolin da yankin yake fuskanta.
Haka nan kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi akan madatsar ruwan kasar Habasha da Masar take da sabani da Addis Ababa akai, da kuma yadda za a fuskanci wannan matsala.
Kasar Sudan dai ta fada cikin yakin basasa ne tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023 wanda ya zuwa yanzu ya ci rayuka da dama da kuma mayar da wasu miliyan 14 zama ‘yan hijira.
Shugabannin biyu na kasashen Masar da Sudan sun kuma tattauna daukar mataki na bai daya akan madatsar ruwan na kasar Habasha. Sun kuwa nuna damuwarsu akan yadda madatsar ruwan na kasar Habasha yake shafar raguwar yawan ruwan Maliya da yake kwararowa a cikin kasashen nasu.