Shugaban Kasar Kamaru Yace Zai Tsaya Takara A Wa’adi Na Takwas

Shugaban Kamaru Paul Biya, ya bayyana cewa zai tsaya takara a wa’adi na takwas a watan Yuli, yana mai kafa hujja da cewa hakan  amsa

Shugaban Kamaru Paul Biya, ya bayyana cewa zai tsaya takara a wa’adi na takwas a watan Yuli, yana mai kafa hujja da cewa hakan  amsa kiraye-kirayen jama’a ne da ke neman ya ci gaba da mulkin kasar.

Duk da sukar da ake yi, da kuma dimbin kalubalen tsaro da tattalin arziki, shugaban kasar da ya fi dadewa kan karagar mulki a duniya na da  damar samun nasara a zaben da za a gudanar a kasar da ke da tsakiyar nahiyar Afirka,  mai arzikin koko da man fetur.

Sai dai watakila babban abin da ke fuskantar Biya a wannan karon shi ne lafiyarsa, wadda aka dade ana ta cece-kuce a kai, musamman yadda ya shafe kwanaki 42 a bara ba a ji duriyarsa ba ko kuma samun wani labari dangane da halin da yake ciki.

Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da batun matsalolin da suka shafi lafiyar shugaban, ta bayyana hakan da cewa wata almara ce kawai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments