Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar Iran nan gaba zai ginu ne bisa shirin  bayan karewar man fetur ne, inda

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar Iran nan gaba zai ginu ne bisa shirin  bayan karewar man fetur ne, inda fasahohi da ilmi da kirkire-kirkire da kuma darussan da za’a dauko daga kasashe kawayen kasar a kungiyoyin BRICS da kuma SCO ne zasu zama  abin dogaru.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto shugaban yana fadar haka  ne a daren jiya Asabar a wani taro wanda yake magana a kan hanyoyin da Iran zata bi don bunkasa fasaha da ilmin kere-keren kasar da samar da ci gaba masu dorewa a kasar. Pezeshkiya yace sauye-suyen da sauri da ake samu a duniya musamman a yankin tekun fariya sun sanya dabarbarun ci gaba na sauyawa da sauri ga kasar Iran.

Ya ce dole ne Iran ta maida hankali wajen samar da dukiya ta hanyar samar da kamfanoni wadanda suka gina ayyukansu kan bincike da ilmi. Mu dauko ilmomin jami’o’immu mu maida su a aikace a cikin kamfanonimmu.

Sanna ya kara da cewa dole ne mu dauki korewar da kasashe mambobi a kungiyoyin BRICS da SCO mu yi amfani da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted