Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada cewa: Shahadar wani jigon gwagwarmaya ba ta yin tasiri a ayyukan gwagwarmaya wajen kalubalantar ‘yan mamaya.
Shugaban na Iran a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Kisan gilla da shahadar jagoran gwagwarmaya kuma shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas Yahya Sinwar, duk da cewa yana da zafi da gadar da bakin ciki ga kowa da kowa a tsakanin ‘yantattu na duniya, musamman ga jaruman al’ummar Falastinu, amma hakan yana nuni ne karara kan ci gaba da tafka laifuffukan da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya suke yi ne da kuma kisan gillar da suke yi wa kananan yara.
Pezeshkian ya kara da cewa: Shahidi Sinwar ya kwashe tsawon shekaru na rayuwarsa mai albarka a hannun ‘yan sahayoniyya masu aiwatar da kisan kai, sannan kuma ya ci gaba da gwagwarmaya har zuwa lokacin karshen rayuwarsa mai daraja, inda ya yi gwagwarmaya ba tare da mika wuya ba ga lalatattun al’umma ba.
Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Jihadi a fagen tunkarar wuce gona da iri da samar da ‘yanci da kuma ‘yanci ga masu mallakin kasa na gaskiya, hanya ce mai girma da kuma manufa madaukakiya da ba za ta tsaya ba don aiwatar da kashe-kashen gilla kan jarumai da shugabanni a wannan fagen.