Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Batun Samun Hadin Kai Tsakanin Al’ummar Kasar

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da kasashen makwabtanta Shugaban kasar Iran Mas’oud

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da kasashen makwabtanta

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa: “Babban burinsu shi ne neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da  makwabtansu, kuma ba su dauke da kiyayya a kansu.”

Shugaba Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a gaban taron majalisar kwararru masu zaben Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a jiya litinin, ya jaddada wajabcin kiyaye hadin kai da hadin kai a cikin kasar da dukkan al’ummar musulmi. Yana mai cewa: “Tare da haɗin kan kasa, za su iya magance dukkan matsalolin cikin gida.” Sannan ya kuma yi kira da a kaucewa duk wani mataki da zai kawo cikas ga wannan hadin kai tare da daukar hanyar kawo sauyi a maimakon fada da juna.

Shugaba Pezeshkian ya ci gaba da cewa: Al’ummun da ke rayuwa a wannan ƙasar, ko da wane irin ƙabila ne, ko jinsi, ko kuma imaninsu, suna da hakkin gudanar da mu’amala a kan tubalin gaskiya da ‘yancin yin adalci da kuma samun adalci daga gwamnati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments