Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake halartar taron brinin Doha, na kasashen musulmi da larabawa, ya gana da sarkin Qatar Tamim Bin Hamad ali-Thani,

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake halartar taron brinin Doha, na kasashen musulmi da larabawa, ya gana da sarkin Qatar Tamim Bin Hamad ali-Thani, inda su ka tattaunawa halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.

Taron na Doha ne na gaggawa ne wanda aka shriya shi, domin tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar Qatar a wani yunkurin yi wa shugabannin Falasdinawa kisan gilla.

A yayin wancan harin dai, ‘yan sahayoniyar sun harba makamai masu linzami fiye da 10 akan wani gini wanda jami’an kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas suke taro a ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted