Shugaban Kasar Ecuador Ya Tsallake Rijiya Da Baya Daga Kisan Gilla

Shugaban kasar Ecuador ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi Ministan Makamashi na Ecuador, Ines Manzano ya sanar a

Shugaban kasar Ecuador ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi

Ministan Makamashi na Ecuador, Ines Manzano ya sanar a ranar Talata cewa: An yi yunkurin kashe shugaban kasar Daniel Noboa kuma an kama wasu mutane biyar da ke da hannu a ciki makarkashiyar.

Manzano ya ce “Motar Noboa na kewaye da gungun mutane kusan 500 da suke jefanta da duwatsu a lokacin da yake tafiya a cikin ayarin motocin zuwa lardin Cañar, inda aka shirya zai sanar da jerin ayyukan samar da ababen more rayuwa.”

Ta kara da cewa: “Daga baya an samu alamun harsashi a motar, amma Noboa bai samu rauni ba a harin.”

Hukumomin kasar sun sanar da cewa: Wadanda ake tsare da su za su fuskanci tuhumar “ta’addanci da yunkurin kisan kai.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments