Shugaban Kasar DRC Ya Kira Yi Takwaransa Na Rwanda  Da Ya Daina Taimakon M23

Shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi ya yi kira ga takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame ya kawo karshen taimakon da kasarsa take bai wa kungiyar

Shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi ya yi kira ga takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame ya kawo karshen taimakon da kasarsa take bai wa kungiyar M23.

Shuagab Tshisekedi ya bayyana hakan ne dai a wurin taron kasa da kasa dangane da zaman lafiya da aka bude a birnin Brussel na kasar Belgium, da shi ma takwaransa na na Rwanda Paul Kagame yana zaune a wurin.

Tsheisekedi wanda yake tsaye yana Magana ya juya da kansa ya kalli Paul Kagame sannan ya ce:

” Ga shugaban Rwanda nan ina gani, kuma da shi nake yin Magana. Ina yin magiya da mu kawo karshen gaba. Ya kamata mu kawo karshen wannan rikicin.”

Haka nan kuma ya  ci gaba da yin Magana kai tsaye da Kagame yana cewa:  Ka bayar da umarni ga kungiyar M 23 da kasarka take goyon bayansu, domin mutanen da su ka kashe sun isa haka.”

Kiran da shugaban na DRC ya yi wa takwaransa na Rwanda a gaban sauran shugabannin kasashen duniya, wanda kuma kafafen watsa labaru suke nunawa kai tsaye, ya sake kwabe alakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Babu wani mayar da martani na kai tsaye da ya fito daga bakin shugaban kasar ta Rwanda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments