Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Watsi Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Masa

Shugaba Gustavo Petro ya ce, ba wai kawai ba ya wata mu’amala ta kasuwanci da Amurka ba ne, ba shi ma da koda dala kwaya

Shugaba Gustavo Petro ya ce, ba wai kawai ba ya wata mu’amala ta kasuwanci da Amurka ba ne, ba shi ma da koda dala kwaya daya a cikin wani asusu na bankunan Amurkan balle a ce an rufe shi.

Gustavo ya kara da cewa; ko kadan ba zai taba rusunawa a gaban Amurka ba, ba kuma zai ja da baya ba.

A jiya Juma’a da marece ne dai Baitulmalin Amurka ya sanar da kakaba wa shugaban kasar ta Columbia takunkumi.

Gustavo ya kuma ci gaba da cewa; Yadda yake fada da yaduwar muggan kwayoyi na shekaru masu tsawo, shi ne ya sa Amurkan ta dauki wannan irin matakin akansa alhali kasarsa Columbia tana taimakawa wajen hana Amurkawan shan hodar Iblis.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya taba zargin takwaransa na Columbia da cewa yana taimakawa wajen yaduwar hodar Iblis, tare da siffata shi a matsayin dillalin muggan kwayoyi.

 Amurka dai ta shiga tsama da Shugaban Columbia ne saboda siyasarsa ta kin jinin HKI da take tafka laifukan yaki a Gaza, bayan da kasarsa ta yanke duk wata alakar diplomasiyya da kasuwanci da ita.

A yayin taron babban zauren MDD a birnin New York, shugaban kasar ta Columbia ya yi kira da a kafa rundunar kasa da kasa domin kare al’ummar Falasdinu da HKI take yi wa kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments