Shugaban Kasar Amurka Yace Kungiyar BRICS ta mutu

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin fito ko haraji 100% na kayakin kasashensu dake shiga kasar Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, maganar shugaban zai kara sabani a cikin kasashen kungiyar, ta BRICS wanda suke ganin Amurka ta mamaye al-amuran tattalin arziki a duniya.

An kafa kungiyar BRICS ne a shekara 2009 kuma kasashen da suka fara kafata sune, Brazil, Russia, India, da kuma China, amma daga baya kungiyar ta kara fadada, inda kasashen Afirka ta kudu, Iran, Habasha, da kuma Hadaddiyar daular Larabawa.

Bayan da kasar Rasha ta karbi shugabancin kungiyar na karba karba, tana son ta aiwatar da shirye-shirye har 250 don karfafa kungiyar.

Trump ya kara da cewa idan kasashen Brics suna son su yi wasa da dalar Amurka duk za’a bugesu da kudaden fito dara-bisa dari.

Yace idan yayi masu hada zasu dawo su roki Amurka ta daukewa masu, sun kashe kungiyar BRICS.

Masana sun bayyana cewa idan Brics ta ci gaba da wanzuwa zata zama barazana ga dalar Amurka a matsayin kudaden da ake ajiya da kuma musayar kudade da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments