Trump Ya Shiga Cikin Sahun Masu Mafarkin Rusa Kungiyar Hamas

Shugaban kasar Amurka ya shiga sahun masu mafarkin zasu rusa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ke Falasdinu Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi

Shugaban kasar Amurka ya shiga sahun masu mafarkin zasu rusa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ke Falasdinu

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kawar da kungiyar Hamas idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, yana mai zargin kungiyar da rashin son cimma matsaya. A halin da ake ciki kuma, fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa; Yana nazarin hanyoyin da Amurka za ta bi domin kwato fursunonin yahudawan sahayoniyya daga Gaza.

Da alama mai shiga tsakani na Amurka ya yanke shawarar jagorantar kai farmakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke kaiwa Gaza, inda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta kawar da kungiyar Hamas. Ya yi ikirarin cewa: Kungiyar Hamas ba ta son cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, yana mai imanin cewa; Hamas ba ta son kawo karshen yakin saboda ta san abin da zai faru bayan ta saki fursunonin da suke hannunta. Wannan bayani ya bayyana aniyar ci gaba da yakin, ko da kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta. Duk da amincewar da Trump ya yi na wahala wajen kwato sauran fursunonin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta jaddada cewa; Trump da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, sun dukufa wajen ganin an sako fursunonin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments