Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin.
A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a kasar, Pezeshkian ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da cewa tana kara habaka, tare da jaddada bukatar gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu, musamman ma cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu.
Ya ce, “Iran da Rasha suna da rawar gani da za su iya takawa domin inganta hadin gwiwarsu, kuma mun kuduri aniyar karfafa huldar dake tsakanin Tehran da Moscow,” in ji shi.
Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da yin cudanya mai ma’ana a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban ya kara da cewa, “Iran da Rasha suna da ra’ayoyi iri-iri kan batutuwan da suka shafi yankin, kuma suna neman karfafa hadin gwiwarsu a matakai na kasa da kasa, ta hanyar huldar dake tsakaninsu, da kuma kungiyoyi irinsu kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kungiyar Eurasia, da BRICS.”
Ministan na Rasha ya kuma jaddada cewa, za a yi duk mai yiwuwa don dorewa da kuma kara habaka wannan hadin gwiwa.
Lavrov ya ce, kammala shigar Iran cikin kungiyar tattalin arzikin Eurasia zai samar da wata sabuwar hanya mai inganci don karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu – musamman a fannin tattalin arziki da cinikayya.