Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Dr. Masoud Pezeshkian, ya isa babban birnin Kazakhstan, Astana, bisa gayyatar takwaransa na Kazakhstan. Mataimakin Firayim Minista na Kazakhstan ya

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Dr. Masoud Pezeshkian, ya isa babban birnin Kazakhstan, Astana, bisa gayyatar takwaransa na Kazakhstan.

Mataimakin Firayim Minista na Kazakhstan ya tarbi Shugaba Pezeshkian a filin jirgin saman Astana. Wannan ziyarar ta zo ne  bisa gayyatar shugaban Kazakhstan, wadda ke da nufin yin tattaunawa ta musamman tsakanin kasashen biyu.

A daya bangaren kuma Jakadan Iran a Moscow, Kazem Jalali, ya sanar da shirin ganawa tsakanin Shugaban Iran Masoud Pezeshkian da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Turkmenistan.

Wannan ya zo ne a lokacin ziyarar da Putin ya shirya kaiwa zuwa Ashgabat a ranakun 11 da 12 ga Disamba don halartar wani taron tunawa da Ranar Zaman Lafiya da Aminci ta Duniya.

Kasashen Iran da Rasha dai sun kara bunkasa harkokinsu an tsaro da ayyukan soji a cikin watannin baya-baya nan, duk da cewa akwai tsohuwar alaka ta soji a tsakanin kasashen biyu, amma dai a halin yanzu alakar tana samun ci gaba a cikin sauri da ba a taba ganin irinsa ba, wanda kuma ake ganin hakan ba zai rasa nasaba da irin halin Rashin tabbas da ake ciki yankin ba, inda kasashen biyu kawayen juna suke yin aiki kafada da kafada domin tukarar duk wani kalubale.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted