Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya fara wata ziyarar aiki a kasar Oman mai manufar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu aminnan juna.
Shugaba Pezeshkian ya yaba da rawar da Oman ta taka a tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka, kuma tana fatan za a cimma sakamako mai kyau.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ya yi da Sultan Haitham bin Tariq na Oman a birnin Muscat a yammacin yau Talata.
Da yake jaddada matsayin kasar Oman a cikin manufofin ketare na Iran, Pezeshkian ya ce Tehran na da cikakkiyar amincewa ga Oman, kuma wannan amana na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaban ya ce Iran a shirye ta ke ta inganta hadin gwiwa da Oman a dukkan fannoni, yana mai imani cewa kasashen biyu suna da karfin da za a iya amfani da su don cin moriyar juna da sauran al’ummomin yankin,” in ji shi.
Ya ce Iran a shirye take ta inganta hadin gwiwa da Oman a fannonin, kimiyya, ilimi, da fasaha, musamman a fannin likitanci.
A nasa bangare Sultan Haitham ya bayyana cewa ya yarda idan aka bude hanyoyin gudanar da harkokin kasuwanci, kasashen biyu za su samu gagarumin ci gaba a huldar dake tsakaninsu.
Dangane da tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka, Sultan Haitham ya ce Muscat ta shiga tsakani a tattaunawar da alheri,” in ji shi.
Sarkin na Oman ya kuma yaba da matsayin Iran na kare al’ummar Falasdinu.