Iran: Mas’ud Pezeshkiyan Ya Isa Birnin Bandar Abbas Dake Kudancin Kasar

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba da ziyarar aiki yi a fadin jihohin kasar, da yake kaddamar da ayyukan ci gaba da aka kammala.

Ziyarar ta shugaban kasa a jihohi tana taimakawa wajen samar da cundanya tsakanin gwamnati da jama’a, kuma tana bawa shugaban kasa dama gane ma idonsa irin kalubalen da ake fuskanta da kuma bada umarnin kawar da duk wani abu da ka iya kawo cikas wajen ayyukan raya kasa.

Gwamnatin iran ta mayar da hankali wajen karfafa damammaki a bangaren ilimi da ci gaban tattalin Arziki a jihohi daban daban, ziyarar lardin Hormuzgan wani bangare ne na babban shiri na cudanya da alummomin yanki da kuma magance matsalolin dake jawo ci baya a yanki.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na kasar ya bayyana irin sakamakon da aka samu a ziyarar jihohi da yake yi,.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted