Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce JMI Bata Da Makaman Nukliya

Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake

Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata,  da kuma fasahar kera makamin idan tana son yin hakan.  

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Agentina a yan kwanakin da suka gabata. Ya kuma kara jaddada cewa a halin yanzu JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana da abinda ake kira “sinadarin Uranium da ta gasa, wanda yawansa zai iya samar da makaman nukliya har zuwa 6-ko 7, amma dai bata kera makamin ba.

Abinda tambaya a nan itace tunda hukumar ta tabbatar da cewa a halin yanzu Iran bata da makaman Nukliya me yasa Amurka take tada hankali kuma take barazana ga kasar dangane da shirin ta na makamashin Nukliya al-hali bata da shi?

Grossi ya bayyana cewa al-amuran siyasa da kuma takurawa kasar da kasashen yamma suke yi shi ne yake ruruta rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da kasashen yamma. Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnatin JMI tana bada hadin kai ga masu binciken hukumar wadanda suke gudanar da bincike a dukkan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar ta Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments