Shugaban Ghana ya ziyarci kasashen Sahel da suka balle daga Ecowas

Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel

Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas.

Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel.

Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin arziki da tsaro.

Kafin Nijar, John Dramani Mahama ya je Mali inda Janar Assimi Goïta ya tarbe shi. A cewar fadar shugaban kasar Ghana, ganawar da aka yi tsakanin mutanen biyu ta ba da damar fara tattaunawa kan karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro.

Shugaban na Ghana ya kuma yi amfani da wannan dama wajen bayyana mahimmancin kasuwanci ta hanyar hanyar tashoshin jiragen ruwa na Ghana da ke Tekun Atlantika ga Mali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments